Shugaba Amurka Joe Biden, ya dauki matakin kare shirin ziyarar da zai kai kasar Saudiyya a mako mai zuwa, wanda ya ce mutane da dama ba su amince da ita ba.
A wani bayani da aka wallafa a jaridar Washington Post, Mista Biden ya ce aniyarsa ita ce inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu, ba tare da ya karya muradun Amurka ba.
Ya ce a bayyane ta ke karara baya goyon bayan cin zarafin dan adam, sannan batun ’yancin bil Adama na daga cikin muhimman batutuwan da za su tattauna da hukumomin Saudiyya.
Ya kafe kan tafiyar zuwa yankin Gabas ta Tsakiya na da muhimmanci, daidai lokacin da ake batun tsadar makamashi da kayan abinci da man fetur sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.