✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Gambiya

Shugaba Adama Barrow ya ce an cafke wasu sojoji hudu da ake zargin su da hannu a yunkurin juyin mulkin na ranar Talata

Gwamnatin Gambiya ta sanar cewa ta yi nasarar dakile wani yunkurin juyin mulki da sojojin kasar suka yi.

Shugaban kasar, Adama Barrow ya sanar a ranar Laraba cewa an cafke wasu sojoji hudu da ake zargin su da hannu a yunkurin juyin mulkin na ranar Talata.

“Mun samu bayanan sirri cewa sojoji na kitsa juyin mulki don barar da gwamnatin Dimokradiyya a Gambia a jiya (Talata), amma mun samu nasarar kama sojoji hudu da ke da alaka da hakan.

“Yanzu haka suna hannun rundunar tsaro kuma mun sa a kamo sauran wasu uku da su ma  muke zargin da hannunsu a lamarin”, in ji Shugaba Adama Barrow.

Duk da cewa babu tabbacin wadanda suka shirya juyin mulkin, bayanan da gwamnatin ta fitar na nuna cewa an samu zirga-zirgar sojoji a kewayen fadar gwamnatin kasar a ranar Talatar, da kuma yaduwar rade-raden yiwuwar aukuwar juyin mulki a daren ranar.