✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda raga-raga a Borno

’Yan ta’adda da dama sun kwanta dama.

Dakarun sojojin Najeriya sun yi wa mayakan ISWAP da na Boko Haram raga-raga a wani samame da suka kaiwa maboyarsu a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

Aminiya ta ruwaito cewa, dakarun da suka hada da sojin sama da na kasa sun kai samamen ne kan tungar ’yan ta’addan da jiragen yaki na sojojin saman kirar Tucano.

Bayanai sun ce mayakan Boko Haram da na ISWAP da dama sun kwanta dama a yankin Darajamal Mayenti da ke Karamar Hukumar ta Bama.

Wata majiya ta dakarun sojin ta bayyana cewa, an yi raga-raga da tungar ’yan ta’addan, inda da aka kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan a ranar Juma’a a sakamakon samamen sojin ta kasa da sama a dajin Sambisa.

Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya tabbatar da faruwar lamarin a karshen makon nan a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Ya bayyana cewa, “Yan ta’addan sun yi mummunar asara, yayin da suke tafiya a cikin ayarin motocinsu masu dauke da bindigogi.

“Akwai kuma wasu kuma a kan babura yayin da wasu kuma samamen ya ritsa da su a sansaninsu da ke cikin dajin na Sambisa.”

Wakilinmu ya ruwaito Zagazola yana cewa, ’yan ta’addan sun yi sansani ne a maboyar Bula Ngufdoye, Ngori, Kote da kuma dajin Tangalanga.

A cewarsa, sauran maboyar sun hada na dazuzzukan Kulo Gomma, Bulamarwaye, Garje, Wuta da kuma yankin Mordo da ke iyaka da kasar Kamaru.

“Jiragen yakin na Tucano sun kai harin bama-bamai a wurare uku da suka kai ga halaka ’yan ta’addar,” in ji shi.

Haka kuma Zagola ya ce an lalata wasu makaman ’yan ta’addan da suka hada da manyan bindigogi.

Ya ce ‘yan ta’addan da suka yi yunkurin tserewa sun sun gamu da hari na jiragen Tucano da ya kai su ga rasa rayukan su.

“Ana amfani da maboyar wajen kai hare-hare a kan sansanin sojoji da kuma wurare masu rauni ta fuskar tsarao a yankin Banki,” in ji shi.

%d bloggers like this: