Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta yi fatali da umarnin Gwamnatin Zamfara ga jama’ar jihar su dauki makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.
Babban Hafsan Tsaro na Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya ce babu hikima a wannan umarnin da Gwamnatin Bello Matawalle ta bayar.
- Abin da muka tattauna da Obasanjo kan 2023 — Farfesa Ango Abdullahi
- ‘Yunwa ta kashe mutum 23 a sansanin ’yan gudun hijira da ke Katsina’
- NAJERIYA A YAU: Irin Shaidar Karatu Da Ake Bukatar Masu Neman Shugabanci Su Mallaka
Ya ce, “Gwamnan ba shi da hurumin ya umarci Kwamishinan ’Yan Sanda ya ba da lasisin [mallakar bindiga].
“Duk da cewa zuwa yanzu ba ni da cikakken bayani sosai, amma ba na tunanin abin da ya yi daidai ne,” inji shi.
Irabor ya yi wannan jawabi ne bayan Gwamna Matawalle ya umarci Kwamishinan ’Yan Sanda Na Jihar Zamfara ya kammala shirye-shiryen fara bayar da takardun iznin mallakar bindiga ga duk wanda yake bukata domin kare kansa a fadin jihar.
A cewar gwamnan, za a ba da takardun neman izinin mallakar bindiga guda 500 ga kowacce daga cikin masarautu 19 da ke fadin jihar domin masu bukata.
Amma a martaninsa, Janar Lucky Irabor ya ce, “Ba daga wurin gwamnoni muke daukar umarni ba, akwai Babban Kwamandan Tsaro na Kasa, wanda shi ne kundin tsarin mulki ya ba wa hurumin sarrafa sojoji, kuma abin da muke yi ke nan a Jihar Zamfara da sauran jihohi, wanda na tabbata bai saba kundin tsarin mulki ba.
“Muna aiki a wadannan jihohi ne domin taimaka wa ’yan sanda a aikinsu domin tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.
Ya ce wannan batu da ba wa duk wanda ke bukata lasisin mallakar bindiga abu ne da ya kamata Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Tarayya wa warware.