Sojojin Najeriya sun sake yin Rugu-Rugu da wasu karin sansanoni 14 na ’yan ta’addan ISWAP a yankin Tafkin Chadi.
Sojojin runduna ta musamman ta 198, sun gudanar da gagarumin aikin ne tare da hadin gwiwar dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF) na kasar Chadi, domin fatattakar ’yan ta’addan a yankin Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
- Masallacin Harami ya karyata bidiyon kiran Sallah daga cikin Ka’aba
- An kama Boka da tawagarsa da ake zargi da kashe ’yar sanda a Imo
- GANI YA KORI JI: Hotunan muhimman abubuwa da suka faru a wannan mako
Wani jami’in leken asiri, ya ya ce yankunan da sojojin suka kwace a hannun mayakan ISWAP su ne Kangarwa, Alagarno, Daban Masara, Kwatan Daban Masara, Grede, Makar, Daban Karfe, Bulawa, Daban Gajere, Kwatan Garba, Ali Sharafti da kuma Tamfalla (kasuwar kifi) daga hannun ’yan ta’addan.
Majiyar ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya, kuma manazarcin harkokin tsaro a yan Tafkin Chadi, cewa an kashe wasu ’yan ta’addar da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da sojojin suka kai farmaki maboyarsu inda da yawa daga cikinsu suka gudu suka bar kayansu.
Majiyoyinmu sun bayyana cewa a ci gaba da kai hare-hare ta kasa da jiragen yaki a yankin, inda dakarun Rundnar Desert Sanity da MNJTF Lake Sanity suka yi ya yi matukar matsin lamba kan mayakan tare da kawo musu na kasu.
A cewarsa, hakan ya faru ne sojojin tare da hadin gwiwar dakarun kawancen kasashen Chadi, Nijar da kuma Kamaru suka yi ta kai hare-hare ta hanyar leken asiri, wanda ya yi sanadin mutuwar yawancin ’yan ta’addar, ciki har da manyan kwamandojinsu da kuma yadda aka shafe matsugunansu gaba daya.
“Yawancin mayakan da iyalansu sun yi watsi da makamansu sakamakon matsanancin matsin lamba da rashin magani ga wadanda suka samu raunuka;
“’Yan ta’addan da suka tsira kuma an tilasta musu tserewa zuwa sansanonin wucin gadi da aka kafa a wuraren da suka mayar mafakarsu.
“Majiyar ta kara da cewa tuni ’yan ta’addan sun garzaya zuwa magudanar ruwa na Daban Masara kuma a halin yanzu suna buya a kananan hukumomin Sabon Tumbu, Tudun Wulgo, Kusuma da Sigir n Marte da Ngala.
Wasu mayakan an gano su a cikin kwalekwale tare da iyalansu yayin da suke kokarin tserewa ta hanyar Kaduna Ruwa da Kandahar da ke tsakanin iyakar jamhuriyar Nijar da Chadi,” in ji majiyar.