A wani lamari da ake kyautata zaton juyin mulki ne a kasar Guinea, yanzu haka dai sojojin kasar na can tsare da Shugaban Kasar, Alpha Conde.
Sojojin Kasar na musamman ne dai suka karbe mulkin kasar ranar Lahadi sannan suka sanar da rushe muhimman hukumomin kasar.
- An sace mata da ’ya’yan dan majalisar Katsina
- NDLEA ta kama mai yi wa kasa hidima da ke safarar miyagun kwayoyi
Ana dai ganin Shugaba Conde a matsayin wani na hannun daman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ko a shekarar 2018 sai da ya gudanar da bikin Sallah tare da Buharin a garin Daura kuma Sarkin Dauran ya yi masa sarautar Talban Daura.
“Mun yanke shawarar cewar bayan dauke Shugaban Kasa wanda yanzu haka yake hannumu…mun rushe Kundin Tsarin Mulki mun kuma rushe hukumomin gwamnati tare da rufe dukkan iyakokin kasarmu na kasa da na sama,” inji daya daga cikin sojojin da suka aiwatar da juyin mulkin a cikin wata sanarwa.
An dai yayata sanarwar a shafukan sada zumunta, amma har yanzu ba a watsa ta a kafafen yada labaran kasar ba.
Masu shirya juyin mulkin dai sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) cewa Shugaba Conde na hannunsu.
Sai dai a nata bangaren, Ma’aikatar Tsaron Kasar ta fada a cikin wata sanarwa cewa “’Yan bindiga sun jefa tsoro a zukatan mazauna birnin Conakry, kafin daga bisani su tunkari Fadar Shugaban Kasa, amma masu gadin fadar, tare da taimakon jami’an tsaro da sauran jama’a sun shawo kan barazanar sannan suka kori maharan.”