Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta tabbatar da faruwar wani hatsarin mota wanda ya rutsa da dakarunta a garin Katuru da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a Jihar Borno.
Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar- Janar Farouk Yahaya, ya jajantawa dakarun da suka yi rauni a hatsarin, a lokacin da ya kai musu ziyara a asibitin da suke murmurewa.
- ‘Manoman auduga 65,000 za su amfana da rancen noma’
- Abin da shugabannin Ibo ke nufi da batun ballewa -Sanata Abdullahi Adamu
Mai magana da yawun rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar.
Nwachukwu ya ce dakarun sun yi hatsarin ne ranar Alhamis yayin da suke kokarin kai dauki don dakile wani farmaki da Boko Haram za ta kai.
A cewarsa, “Daya daga cikin manyan motocin sojin ce ta kauce hanya sannan ta haddasa hatsarin.”
Ya ce dakaru tara daga cikin sojojin sun yi rauni, kuma tuni aka dauke su zuwa asibitin sojoji inda suke murmurewa.
“Babu wanda ya rasa ransa a hatsarin.
“Janar Yahaya ya jinjina musu kan yunkurin da suka yi na kai dauki don agajin gaggawa,” a cewarsa.