Wasu jami’ai da ake kyautata zaton na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ne sun yi awon gaba da Shugaban Hukumar Kula da Gyaran Hanyoyi ta Jihar Katsina (KASROMA), Injiniya Yazid Abukur.
Rahotanni sun ce jami’an sun yi wa Shugaban dirar mikiya lokacin da yake tsaka da cin abinci a wani wajen sayar da abinci na filin jirgin sama na Umaru Musa ’Yar’aduwa da ke Katsina.
- Harin da aka kai min ya saba yarjejeniyar zaman lafiya —Atiku
- ’Yan bindiga sun kashe malamai 2,000 a shekara 8
Daga nan ne kuma bayanan suka ce an lullube shi da bakar hula, sannan aka tafi da shi wurin da har yanzu babu wanda ya iya tantancewa.
Babu dai wata majiya daga hukumar sojojin ko iyalan shi Injiniyan da ta magantu a kan lamarin, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kakakin Rundunar Yansanda na Jahar Katsina, SP Gambo Isa, ya ce ba su da wata masaniya a kan wannan kamun.
Kamun Injiniyan dai na dauke da alamomin tambaya da dama domin an ce sojojin ba su cika kama mutane haka kawai ba.