Sojoji masu juyin mulki a kasar Mali sun tsare Shugaba Ibrahim Boubakar Keïta bayan kwace iko a kasar.
Wani Kakakin gwamnatin kasar ya ce sojojin da suka yi ta harbe-harbe sun kuma yi awon gaba da Firaminista Boubou Cissé duk da cewa a baya ya yi kira da a yi tattaunawa ta fahimta.
Yunkurin juyin mulkin ya fara ne a safiyar Talata inda sojojin suka yi ta harbe-harbe a wani sansani a garin Kati da ke kusa da Bamako, babban birnin kasar.
A ranar ce kuma gungun wasu matasa masu zanga-zanga suka cinna wa gine-ginen gwamnati wuta a yayin zakaga-zangar kin jinin gwamnati a Bamako.
Gabanin nan sojoji sun tayar da tarzoma a babban barikin na Kati inda suka kame tare da kukkulle manyan hafsoshi a kwamandojinsu suka kwace iko.
Tuni dai Tarayyar Afrika da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) da kasar Faransa da ta yi wa Mali mulkin mallaka suka la’anci juyin mulkin.
Matakin da sojojin kasar suka dauka ya zo ne a yayin da ake ta gangamin gudanar da zanga-zangar neman Shugaba Keita ya yi murabus.
‘Yan kasar na zargin shugaban da gaza magance matsalar tsaro da durkushewar tattalin arziki baya ga yawaitar cin hanci da rashawa.