Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun halaka mayaƙan Lakurawa da dama tare da lalata sansanoninsu guda 22 a Jihar Sakkwato.
Babban Kwamandan Rundunar Soji ta 8 kuma Kwamandan Rundunar Operation Fansan Yamma, Birgediya-Janar Ibikunle Ajose ya cewa sojoji sun ƙwato makamai da dama daga hannun ’yan ta’addan da suka halaka.
A ranar Juma’a ne Birgediya-Janar Ibikunle Ajose ya sanar da haka a jawabinsa ga dakarun runduna ta musamman da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa ya kafa domin murƙushe Lakurawa a jihohin Sakkwato da Kebbi.
Ya bayyana musu cewa kafin zuwansu, sojojin Runduna ta 8 da Operation Fansan Yamma sun tarwatsa sansanonin Lakurawan da ke da “Rumji Dutse da ke Gabashin Sarma, sai kuma Tsauna da Bauni, Malgatawa, Gargao, Tsauna da Dajin Magara, Kaideji, Nakuru, Sama, Sanyinna, Kadidda, Kolo da ƙauyukan Dancha da ke kananan hukumomin Illela, Tangaza da Binji.
“Haka ya yi sanadin lalata sansanoni 22 na Lakurawa da kashe wasu daga cikinsu, tare da ƙwato bindigogi da wasu makamai da dama,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa rundunar da aka kafa za ta ƙara ƙarfin sojoji wajen murƙushe ’yan ta’adda a jihohi yankin Arewa maso Gabas da ke fama da matsalar tsaro.
Ya ci gaba da cewa, “zuwanku zai kara ƙarfin dakarun wajen fatattakar Lakurwa daga dazuka.”
Don haka ya buƙaci kada su sassauta wa Lakurwa, kuma su nuna ƙwarewa wajen kare rayuka da dukiyoyin fararen hula.
Ya shaida musu cewa an zaɓo su ne aka ba su horo na musamman domin wannan aiki, kuma ’yan Nijeriya na da ƙwarin gwiwa cewa za su ga bayan Lakurawa, don haka su ba maraɗa kunya.