Sojojin sun kai samame a wasu gidajen karuwai masu karancin shekaru da ke Kasuwar Fara a Rukunin Gidajen Shagari Masu Saukin Kudi da ke Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
Rufe gidan karuwan ya biyo bayan wani rahoto na musamman da jaridar Daily Trust ta yi a ranar Asabar da ta gabata, inda ta bankado yadda ake tafka ta’asa a gidajen karuwai.
- Za a sa kyamarorin tsaro na N495m a tashoshin jirgin kasan Abuja-Kano
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabon Tsarin CBN Zai Raba Mutane Da Ayyukansu
Mazauna yankin sun ce an kuma kama wasu mutane bayan “Sojoji sun kai samame wurin kwanaki biyu da suka wuce.
“Ba mu san inda suka kai masu laifin ba,” in ji wata mazauniyar yankin mai suna Halima Abdul.
Ta ce samamen da kuma sintiri da sojoji suka yi a yankin ya sanya al’umma cikin kwanciyar hankali.
“Mun sha wahala tsawon shekaru ana azabtar da mu amma da abin da muke gani yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu,” in ji ta.
Wani mazaunin yankin, Solomon Joseph, ya ce samamen da dakarun suka kai abin yabawa ne.
“Akwai ’yan kasuwa da suke sana’arsu a Kasuwar Fara, muna rokon sojoji da su bar su su dawo su ci gaba da harkokinsu,” in ji shi.