Dakarun Rundunar Sojin Najeriya ta 13 da ke Kalaba ajihar Kuros Riba sun mika wasu mutane uku da suka cafke wadanda kuma ake zarginsu da aikata fashi da makami ga ’yan sanda don ci gaba da gudanar da bincike.
Kwamandan Rundunar, Manjo Stanley Ikpeme ne ya mika wadanda ake zargin a madadin Babban Kwamandan Rundunar ta 13, Birgediya Janar Mohammed Abdullahi, a barikin Birged na birnan Kalaba a Juma’a.
- An zargi soja da kisan yaro saboda Mangoro a Kaduna
- Kotu ta dakatar da shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano
- ‘Mun kama soja dumu-dumu yana ba ’yan ta’adda kaki da albarusai’
Ya ce an cafke mutane ukun ne yayin da jami’an rundunar soji ta “Operation Akpakwu,” ke gudanar da sintiri a Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu ranar 14 ga watan Febarairun da ta gabata.
An dai kama wadanda ake zargin ne dauke da karamar bindigar pistol kirar gida.
Manjo Ikpeme ya ce an sha kama daya daga cikinsu a wurare da aka aikata fashi da dama a yankin Kalaba ta kudu.
A nasa bangaren, Mataimakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Igri Ewa wanda ya karbi mutanen ya ce rundunar zata shiga bincike kan lamarin ba tare da bata wani lokaci ba.