✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Dakarun sun ceto wasu mutum bakwai da mahara suka sace.

Rundunar Sojin Najeriya, ta sanar da nasarar lalata sansanin ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji, da wasu sansanoni a yankin Fakai na Ƙaramar Hukumar Shinkafi, a Jihar Zamfara.

Wannan samame ya faru ne a ranar 10 ga watan Janairu, 2025 a cewar wata sanarwa da rundunar sojin ‘Operation Hadarin Daji’ ta fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun sun samu nasarar kai farmakin ne tare da goyon bayan jiragen yaƙin rundunar sojin sama.

Dakarun sun lalata sansanonin wasu gawurtattun ‘yan bindiga da suka haɗa da Bello Turji da Mallam Ila.

“Mun lalata sansanonin ’yan bindiga a yankin Fakai, ciki har da na Bello Turji da Mallam Ila.

“Mun kashe ‘yan bindiga 25 tare da raunata wasu sama da 18,” in ji sanarwar rundunar.

Hakazalika, dakarun sun samu nasarar kuɓutar da mutum bakwai da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Har ila yau, dakarun sun ƙwace makamai da ƙarin kayan aiki daga maɓoyar.