Rundunar sojin saman Najeriya ta kashe mayakan kungiyar ISWAP da dama tare da lalata wata masana’antarsu ta kera abubuwan fashewa a kusa da yankin Tafkin Chadi.
Hare-haren wadanda Manjo Janar Ibrahim Ali, kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas ne ya jagoranta.
- ‘Maniyyatan Kano 156 sun sayi kujerun Aikin Hajji na bogi’
- HOTUNA: Gini ya kashe mai ‘dibar ganima’ a Kano
An kuma yi amfani da jiragen yaki wajen kai harin a ranar Laraba a Tumbun Bakkassi, daya daga cikin wuraren da aka gano ’ya ta’addan na amfani da su wajen kera bama-bamai. .
Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa hukumar leken asiri ta bankado cewa ISWAP ta shirya tare da ajiye ababen fashewa tare da bayyana aniyar tura su a wurin sojoji dake Arege a Karamar Hukumar Abadam.
Wata majiyar sojan ta bayyana cewa harin na daga cikin hare-haren ramuwar gayya da tsojojin suka kai ta sama kan ’yan ta’addan bayan yunkurinsu na kai hari a sansanin sojojin Najeriya da ke Mallam Fatori.
Kazalika, bayanai sun nuna cewa wani jirgin saman sojojin da ke karkashin rundunar sojojin sama na Operation Hadin Kai ya kai wasu hare-hare ta sama a kan wuraren da ’yan ta’addan ke da sansani a Tumbun Shittu da ke kusa da Tafkin Chadi wanda aka tabbatar da samun nasara sosai yayin da aka kuma halaka ’yan ta’adda da dama.
Tun daga ranar 6 ga watan Yunin 2023, rundunar sojojin saman Najeriya ta fara kai hare-hare ta sama a yankin Arewa maso Gabas a karkashin shirin da ake yi wa lakabi da: OPERATION WARUN 3, wanda ya yi sanadin kawar da ’yan ta’addan Boko Haram fiye da dari, kwamandojin runduna da manyan mayaka a tsaunin Mandara a Karamar Hukumar Gwoza.