✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 6 a Borno

An kashe su ne yayin wani harin kwanto-bauna a garin Bama

Sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar yan banga sun kashe mayakan Boko Haram shida a wani samame da suka kai a kasuwar Daula da ke Karamar Hukumar Bama ta jihar Borno.

Dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai (OPHK) ne suka sami nasara a harin.

Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro cewa an kai harin ne da safiyar Juma’a.

Majiyar ta ce sojojin sun yi wa ’yan ta’adda kwanton-bauna ne wadanda galibi ke zuwa kasuwar da ke da nisan kilomita kadan daga yammacin garin Bama domin yin mu’amala da wasu kungiyoyin ta’addanci.

“An ce sojojin sun yi wa ’yan ta’addan kwanton-bauna ne kafin su yi artabu da su inda hudu daga cikinsu suka samu raunuka a sakamakon fadan da aka yi da ’yan  bindigar,” inji majiyar leken asirin.

Haka nan dakarun na OPHK sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 da kekunan hawa guda bakwai a yayin gumurzun.