Babbar hedikwatar tsaro ta Najeriya DHQ, ta sanar da kashe ’yan ta’adda 950 na Boko Haram da mayakan ISWAP da ’yan bindiga cikin watanni bakwai da suka gabata.
Sanarwar ta ce, dakarun Najeriyar sun samu nasarorin ne a yayin farmakin da suka kaddamar kan ’yan bindiga a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya tsakanin watan Mayu na shekarar 2021 zuwa Janairun shekarar da muke ciki ta 2022.
- Rikicin Mali: Jonathan ya ziyarci Buhari
- ’Yan sanda sun cafke dillalan miyagun kwayoyi biyu a Jigawa
Mukaddashin shugaban sashen hulda da jama’a na sojin Najeriya, Manjo Janar Bernard Onyeku, ya fadi hakan ne yau Alhamis a lokacin da yake yi wa manema labarai karin bayani game da ayyukan rundunar sojin kasar a birnin Abuja.
Onyeuko ya ce a karkashin Operation Hadarin Daji, dakarun Najeriya sun yi nasarar kashe ’yan bindiga 537 da sauran masu aikata laifuka tare da kama wasu miyagun mutane 374 da suka hada da ’yan fashin daji da abokan huldar su.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron ya kara da cewar sojoji sun kuma ceto mutane 452 da aka yi garkuwa da su tare da kwato makamai iri-iri har guda 227, da suka hada da bindigogi kirar AK-47, da harsasai fiye da dubu 4, da kuma kwato dabbobi 3,250 da aka sata duk a karkashin farmakin rundunar ta Operation Hadarin Daji.
Janar Onyeku ya ce daga cikin yan ta’addan da aka kashe har da shugabannin ’yan fashin daji Alhaji Auta da Kacalla Ruga.
Manjo Janar Onyeuko ya ce rundunar sojojin sama ce ta samu wannan nasara a ranar 3 ga watan Janairu, lokacin da ta kai farmaki ta sama kan ’yan bindigar da ke dajin Gusami da kuma kauyen Tsamre ta Yamma a Karamar Hukumar Birnin Magaji ta Zamfara, lamarin da ya kai ga halaka ’yan bindiga da dama a sansanonin jagororin ’yan fashin guda biyu.
Game da kisan jagororin ’yan fashin, Janar Onyeku ya ce: “An samu nasarar a ranar 3 ga watan Janairun 2022 bayan samun bayanan sirri da ya bayyana wuraren buyan shugabannin ’yan fashin biyu Alhaji Auta da Kacalla Ruga, inda aka kashe ’yan fashi kusan 100 yayin fafatawar.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Janar Onyeku yana cewa, ’yan ta’adda 79 sun shiga hannu a yayin da kuma sojojin sun ceto fararen hula 113 da aka sace a tsawon wannan lokaci.