✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 44 a Arewacin Najeriya

An kashe su ne a sassan Arwacin Najeriya da dama

Akalla ‘yan ta’adda 44 ne dakarun rundunonin tsaro na Operation Hadin Kai da Hadarin Daji suka kashe cikin mako biyu a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kazalika, dakarun sun samu cafke sama da ‘yan ta’adda 50 a yankunan a tsakani makonnin biyu.

Daraktan Sashen Yada Labarai na Hedkwatar Tsaro da ke Abuja, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da suka saba shiryawa na mako-mako a Abuja ranar Alhamis.

Danlami ya ce, tsakanin 20 ga watan Oktoba zuwa 2 ga watan Nuwamba, dakarun Operation Hadin Kai sun kama wasu mutum 27 da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne, sannan sun kwantar da 19.

Ya kara da cewa, yayin gumurzun, jami’ai sun sun kwace tarin bindigogi da alburusai da sauran kayayyaki masu yawa daga ‘yan ta’addan.

Ya ce nasarorin da suka samu hadin gwiwa ne tsakanin sojojin kasa da na sama inda suka fatattaki ‘yan ta’addan a yankunan da lamarin ya shafa.

(NAN)