Kazalika, dakarun sun samu cafke sama da ‘yan ta’adda 50 a yankunan a tsakani makonnin biyu.
- Ambaliyar ruwan bana ta fi yi wa Jigawa barna fiye da kowace jiha – Minista
- Sayar da matatun mai: Har yanzu ina nan a kan bakata – Atiku
Daraktan Sashen Yada Labarai na Hedkwatar Tsaro da ke Abuja, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da suka saba shiryawa na mako-mako a Abuja ranar Alhamis.
Danlami ya ce, tsakanin 20 ga watan Oktoba zuwa 2 ga watan Nuwamba, dakarun Operation Hadin Kai sun kama wasu mutum 27 da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne, sannan sun kwantar da 19.
Ya kara da cewa, yayin gumurzun, jami’ai sun sun kwace tarin bindigogi da alburusai da sauran kayayyaki masu yawa daga ‘yan ta’addan.
Ya ce nasarorin da suka samu hadin gwiwa ne tsakanin sojojin kasa da na sama inda suka fatattaki ‘yan ta’addan a yankunan da lamarin ya shafa.
(NAN)