✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 75

Rundunar tsaro ta Operation Lafiya Dole ta bindige ’yan Boko Haram 75 tare da rasa dakarunta uku a wata arangamar da suka yi da ’yan…

Rundunar tsaro ta Operation Lafiya Dole ta bindige ’yan Boko Haram 75 tare da rasa dakarunta uku a wata arangamar da suka yi da ’yan tada kayar bayan a yankin Arewa maso Gabas.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi Daraktan Watsa Labarai na Rundunar, Birigediya Benard Onyeuku ya fitar ranar Talata a Maiduguri.

“An kirkiri rundunar Operation Fire Ball karkashin jagorancin Operation Lafiya Dole, domin ci gaba da yaki da ’yan ta da kayar baya na ISWAP da Boko Haram.

“An samu wannan nasarar ne a artabun da aka yi da ’yan ta da kayar bayan ISWAP da Boko Haram, sai dai wasu daga cikin jami’anmu sun rasa rayukansu.

“A ci gaba da dakile hare-haren ’yan ta da kayar bayan an samu nasarar kashe ’yan Boko Haram da ’yan kungiyar ISWAP.

“An samu makamai da dama ciki har da gurneti guda 36, harsasai, motoci masu feshin wuta da makamai iri daban-daban.

Ya kara da cewa mazauna yankin Arewa maso Gabas sun tabbatar da za su ba wa jami’an tsaro hadin kai wajen ba da bayanan maboyar ’yan Boko Haram da ’yan ta da kayar bayan ISWAP.