Rundunar tsaro ta hadin guiwa sun kashe wasu ’yan Boko Haram shida tare da kama wasu da dama, a wani sumame da suka kai wata haramtacciyar kasuwar ’yan ta’adda a Karamar Hukumar Bama a jihar Borno.
Wani kwarrare a harkar tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya shaida wa wakilinmu cewa, ana tsaka da hada-hada ne a kasuwar sojojin suka dirar mata a a safiyar Laraba.
- Bayan shekaru 2, an cafke wadanda suka kashe Dan Majalisar Bauchi
- Buhari Ya Jinjina Wa Sarkin Musulmi Kan Wanzar Da Zaman Lafiya
Ya ce ganin tawagar tsaron ne ya sa ’yan ta’addan suka bude wuta, sai dai ba su samu nasarar kashe kowa ba, sai ma mutum shida daga cikinsu da aka kashe.
Tuni dai aka mika su hedikwatar rundunar tsaron da ke Bama domin ci gaba da bincike.
Haramtacciyar kasuwar da ake kira Daula dai, na kauyen Bararam, kuma ana cinikin kayayyaki ne da suka hada da kayan abinci da miyagun kwayoyi da gwanjon sutura da man fetur.
Bincike ya kuma nuna cewa ’yan ta’addan da ke gudanar da ita na bada kayan ne don musaya da karafuna.