Wani jirgin yakin sojin saman Najeriya samfurin Super Tucano ya kashe ’yan ta’addan Boko Haram 16 a yankin Banki da ke kan iyaka da Karamar Hukumar Bama a jihar Borno.
An halaka ’yan ta’addan ne a ranakun 16 da 17 ga watan Nuwamba, 2022, bayan harin sama da rundunar leken asirin sojojin saman suka yi a yankunan na kan iyaka da kasar Kamaru.
- Gine-gine a kan layin wuta ne ya hana inganta lantarki a Kano — Minista
- Qatar 2022: Fitattun ’yan wasa 10 da suka koma ’yan kallo
Wani kwararre a fannin yaki da tayar da kayar baya, a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, a karshen mako a Maiduguri, ya ce, “Boko Haram ta sake samun wata mummunan asara a aikin hadin gwiwa na sojojin hadin gwiwa a yankunan Banki.”
A cewarsa, ’yan ta’addan da aka kashe suna da matsuguni ne a yankunan Chongolo da Tangalanga da ke kan iyaka da Kamaru, mai tazarar kilomita 134 daga gabashin Maiduguri, babban birnin jihar.
Dangane da yadda aka kashe ’yan ta’addan, ya ce: “Bama-bamai daga harin da jirgin Super Tucano ya kai daidai wurin,” ya kara da cewa hakan ya kai ga halaka 16 daga cikin ’yan ta’addan da baburan su na hawa.
Ya kara da cewa an gudanar da wannan samame ne bisa wasu sahihan rahotannin sirri da ke nuni da cewa matsugunin na daya daga cikin wuraren da mayakan ke amfani da su.
“’Yan ta’addan sun yi amfani da matsugunan ne a matsayin wuraren da suke yin shiri kafin kai hari kan sansanonin soji da ke kusa da su da kuma wurare masu nisa a yankunan Banki da Kamaru,” inji shi.