Akalla ’yan ta’addan Boko Haram 100 ne suka mutu a wani harin sojojin Najeriya da suka kai da jiragen yakin Super Tucano a tsaunin Mandara na Jihar Borno.
Wata kwakkwarar majiya ta sanar da cewa, an kai harin ne da bama-bamai ta sama na tsawon mako guda a Karamar Hukumar Gwoza da ke kan iyaka da kasar Kamaru.
- Gbajabiamila ya yi murabus daga shugabancin majalisar wakilai
- Canjin Dala ya kai N750 a bankunan kasuwanci
Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana, a ranar Litinin, a Maiduguri cewa, an yin amfani da bayanan sirri da ya jagoranci kai hare-hare ta sama tsakanin 9 zuwa 11 ga watan Yuni, 2023 a yankunan Hrazah da Wa-Duhwedeh.
Kazalika, wata majiyar soji a Maiduguri, ta kuma tabbatar da cewa yankuna biyu ne wuraren haduwar ’yan ta’addan, kafin su kaddamar da hare-hare a Gwoza da sauran al’ummomin kan iyaka.
Ya kara da cewa harin da kwararru matuka suka kai ta sama ya yi sanadin kashe wasu kwamandojin na Boko Haram da dama.
Makama ya kara da cewa an kuma kashe manyan ’yan ta’adda, yayin da wasu suka gudu da raunuka sakamakon tashin bama-bamai.
Ya ce a ranar 11 ga watan Yuni, 2023, Rundunar Sojan Sama ta kai hare-hare ta sama kuma ta tabbatar da samun nasara saboda an kashe ’yan ta’adda da yawa tare da barin wasu cikin munanan raunuka.
Rundunar ta kuma lalata gine-gine da dama wadanda ’yan ta’addan na Boko haram suke amfani da su a matsayin maboya.
Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshall IO Amao, ya tabbatar da cewa, an kaddamar hare-hare iri da ake yi wa lakabi da: Operation Warun III, a karkashin rundunar ta Operation Hadin Kai ta hanyar amfani da jiragen saman yaki a matsayin babban abin da aka mayar da hankali akai.