Rundunar sojojin kasa a Jihar Filato, ta ce an gano gawarwakin ’yan bindiga guda takwas bayan harin da ‘yan ta’addan suka kai a wasu sassan Karamar Hukumar Kanam da ke jihar.
Jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Safe Haven’ a jihar, Manjo Ishaku Takwa, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Jos ranar Talata.
- Babbar Sallah: Masarautar Katsina ta soke Hawan Daushe
- Ba ma goyon bayan haramta mana sayar da giya – Masu wuraren shakatawa a Abuja
Manjo Takwa ya tabbatar da cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne a kauyen Angwan Bashar da kuma wani kauye da ke kusa.
“Sai dai da alama ’yan ta’addan ba su ji da dadi ba, don kuwa sojoji tare da hadin gwiwar ’yan banga a yankin sun kashe mutum takwas daga cikinsu sakamakon dauki-ba-dadin da aka yi.”
A cewar Takwa, “Jiya [Litinin] da daddare ‘yan fashin daji sun kai hari Angwa Bashar cikin Karamar Hukumar Kanam.
“Kafin dakarunmu su isa wurin, an rigaya an soma musayar wuta tsakanin ‘yan bangan yankin da ’yan ta’addan. Don haka sojojin suka hada karfi da ’yan bangan suka fatattaki ’yan bindigar.”