✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 4 a Kaduna

An kwace makamai da babura shida a hannun ’yan bindigar

Sojojin Najeriya sun kashe wasu ’yan bindiga hudu tare da kwace bindigogi da alburusai a samamen da suka kai mabuyar ’yan ta’addan a Kaduna.

Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Runduna ta 1, Laftanar-Kanar Musa Yahaya, ya bayyana haka a cikin sanarwar, inda ya ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun tsere da raunukan harbi.

A cewar Yahaya, “Samamen bangare ne na ci gaba da yaki da ta’addanci da garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a Shiyyar Arewa ta Yamma.

“Sojojin Runduna ta 1 da wasu sojojin sama na ‘Operation Whirl Punch’ ne suka fatattaki ’yan bindigar,” in ji shi.

Ya kara da cewa, samamen wanda aka shafe sa’o’i 48 ana fafatawa ya samar da sukuni a hanyoin Manini-Kuriga da Farin Ruwa da Kwanan Yashi da Makera da Dogon Dawa-Maidaro da dajin Kidanda-Yadi da kuma Sabon Birnin, baki dayansu a cikin Karamar Hukumar Birnin Gwari.