Dakarun sojin rundunar Operation Whirl Stroke (OOWS), ta yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga hudu a yayin wata musayar wuta da suka yi a Karamar Hukumar Katsina-Ala da ke Jihar Benuwe.
Haka kuma a wani samame na daban dakarun sojin suka kai a ranar Lahadi, sun kubutar da wani magidanci da matarsa mai juna biyu daga hannun wadanda suka sace su a Karamar Hukumar Guma.
- Mutum 4 sun mutu sanadiyyar rushewar bene mai hawa 3 a Legas
- Rikicin Ukraine na iya rikidewa zuwa Yakin Duniya na Uku — Rasha
Aminiya ta tattaro bayanai daga karamar hukumar cewar, ma’auratan an sace su da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi, amma bayan samun kiran neman agajin gaggawa dakarun suka dukufa har sai da suka ceto su.
Rahotanni sun bayyana yadda dakarun sojin da ‘yan bindigar suka shafe tsawon lokaci suna musayar wuta a tsakaninsu wanda daga bisani sojojin suka samu galaba a kan ‘yan bindigar.
Bayan kashe ‘yan bindiga hudu da dakarun suka yi, sun kuma samu nasarar cafke wani matashi mai shekara 15 a duniya da ke aiki da ‘yan bindigar.
Sai dai kakakin ‘yan sandan Jihar Benuwe, DSP Catherine Anene, ba ta amsa wayarta ba domin jin ta bakinta dangane da faruwar lamarin.