✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan bindiga sun kwato mutum 23

Sojoji sun hallaka ’yan bindiga uku tare da ceto mutum 23 a jihohin Katsina da Zamfara

Rundunar tsaro ta Operation ٍSahel Sanitry ta hallaka ’yan bindiga uku tare da ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara.

Mai Mukaddashin Daraktan Yada Labaran Rundunar, Birgediya Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan ranar Lahadi.

Ya kuma ce wasu ’yan bindigar da dama kuma sun tsere da raunuka daban-daban a jikinsu sakamakon karon-battar da suka yi da su a garuruwan Dankar, Kandawa, Yau-yau, Hayin Yau yau, Bugaje, Zandam, Kwari Mai Zurfi, Yar Gamji, Bukuru da Jibiyawa a kananan hukumomin Batsari da Jibiya a Jihar Katsina.

Birgediya Janar Benard ya ce, “Kazalika, a wani hari da muka kai bayan samun bayanan sirri, mun sami cafke mutum hudu da ake zargin ’yan bindiga ne a kauyukan Kankara da Tudu da ke Karamar Hukumar Kankara ta jihar Katsina.

“Wani wanda ake zargin mai safarar miyagun kwayoyi ne shi ma ya shiga hannu a kauyen Jangebe na yankin Wanki a Karamar Hukumar Gusau da fakiti 20 na allurar Pentazocine da aka boye a cikin babur a lokacin da yake kokarin kaiwa wani kauye mai suna Kungurmi.

“Bincikenmu ya gano cewa mutumin shi ne yake yi wa ’yan bindigar da ke cikin dazuka safarar miyagun kwayoyi.

“Ita ma rundunar da aka jibge a garin Magami ta ceto mutum 23 da aka yi garkuwa da su daga hannun ’yan bindiga da ke kokarin tserewa su bar su saboda karon da suka yi da dakarunmu suna dab da kai wa maboyarsua hari a kan hanyar Zauni zuwa Jangebe a Karamar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara.

“Bincikenmu na farko-farko ya gano cewa an yi garkuwa da mutanen ne a kan hanyarsu ta zuwa Kasuwar Magami daga birnin Gusau a wata motar haya”, inji Birgediya Benard.

Ya ce tuni rundunar ta sada wadanda aka ceto din da iyalansu yayin da kuma ake ci gaba da kokarin sake ganowa tare da tarwatsa bata-garin daga maboyarsu.