Sojojin Najeriya sun kashe mayakan ISWAP guda 19 bayan ’yan ta’addan sun yi musu kwanton bauna a garin Gamboru Ngala da ke kan iyakar Najeriya Jamhuriyar Kamar.
Ragargazar da sojojin tare da ’yan sa-kai Civilian JTF suka yi wa ’yan ta’addar a ranar Litinin a garin mai nisan kilomita 828 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ita ce ta biyu a cikin kasa da kwana uku.
- Shugaban Chadi ya nada tsohon abokin adawar mahaifinsa Fira Minista
- Gasar Zakarun Turai: Fashin baki kan wasannin ranar Talata
- Saudiyya ta sahale wa mata sauke farali ba tare da muharrami ba
Wata majiyar tsaro ta ce, da farko zugar mayakan dauke da muggan makamai sun bude wa sojojin wuta, “Amma dakarun suka fatatte su, suka kuma bi su suka kashe 19 daga cikinsu, amma ba su kashe soja ko daya ba, in banda wasu biyu da suka samu rauni.”
Majiyar ta ce bayan artabun na kusan minti 40, sojojin sun kwace bindigogi kirar AK 47 guda tara da harsasai da mota a-kori-kura guda daya da babura guda tara wadanda ’yan ta’addar suka tsere suka bari.