✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 15 a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ISWAP 15 a wata musayar wuta a yankin Banki na Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno.

Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’addan ISWAP fiye da 15 a wata musayar wuta a yankin Banki da ke Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno.

’Yan Boko Haram din sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da Bataliya ta 151 tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task a rundunar Operation Hadin Kai suka far ma maboyarsu a kauyen Gauri a ranar 30 ga watan Oktoba.

Wata majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, cewa sojojin sun kama wasu daga cikin mayakan na Boko Haram da ke gabar tekun.

Majiyar ta ce dajin ya kasance maboyar ’yan ta’addan da suka shirya kai hari kan sansanonin sojoji ke kusa da su sannan kuma wasu ’yan ta’addan na amfani da wuraren wajen boye dabbobin da suka sato.

Ya ce ayyukan sintiri da sojojin suke yi a yankin na samun nasara, yayin da ’yan ta’addan ke shan kashi, aka hallaka wasu, wasu kuma suka tsere da munanan raunuka.

“An kashe fiye da 15 daga cikinsu nan take,” in ji majiyoyin da suka shiga yakin.

Ya ce “An tilastawa ‘yan ta’addan janyewa tare da jikkata wasu da dama da suka yi barna da sace dabbobi da dama daga hannun mutane.

Ya ce, duk da haka, ’yan ta’addan da suka tsere sun kira ’yan uwansu da su kawo musu dauki a yayin da sojojin ke ci gaba da fatattakar su.

“Da misalin karfe daya da rabi na rana, ’yan ta’addan sun tura karin wasu mutane kan babura, suna ta kururuwar Allahu Akbar, amma sojojin suka yi gaggawar kama su, suka ci karfinsu bayan wani kazamin fada da suka yi.

“Mun kashe karin 7 daga cikinsu a yakin da ya gudana kuma abin takaici, mun rasa jami’an sojanmu guda biyu tare da raunata wasu biyar yayin da muke bin ragowar ’yan ta’adda da suka tsere bayan arangamar.”

Idan dai za a iya tunawa, sojojin Brigade na 21 sun zafafa kai hare-hare kan kungiyar Boko Haram, ta amfani wasu hanyoyin dabarun yaki

’Yan ta’addan sun yi mummunar asara na mutanensu a wani samame na sama da na kasa a karkashin jagorancin rundunar Operation Hadin Kai a ranar Juma’a 27 ga watan Oktoba, a yankin Darajamal da Mayenti.