Rundunar Sojin Sama ta Najeriya NAF ta samu nasarar kashe wasu kwamandojin kungiyar ta’adda ta ISWAP uku a Jihar Borno.
Wakilinmu, rundunar Operation Hadin Kai ta rundunar sojin saman ce ta yi wa mayakan da dama ruwan wuta a garin Marte da Kukawa da ke Kudancin jihar ta Borno.
- Hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan zaben gwamnoni ya ɗaga martabar dimokuraɗiyya — Atiku
- Yadda harin sojoji ya sauya rayuwar mutanen Tudun Biri a Kaduna
Wata majiya ta shaida wa Zagazola Makama, kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi cewa, kwamandojin ISWAP da suka bakuncin lahira sanadiyyar harin sun hada da Abou Maimuna da Abou Zahra da kuma Kwamanda Saleh.
Bayanai sun ce tun a ranar 10 ga watan Janairun da muke ciki ne rundunar sojin ta kaddamar da wadannan hare-hare masu tasiri karkashin jagorancin Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai, Air Commodore UU Idris.
Aminiya ta ruwaito cewa, an samu nasara kan mayakan ne yayin da wani jirgin leken asiri na rundunar sojin ya hango ‘yan ta’addan na tafiya a cikin kwale-kwale.
Majiyar Zagazola Makama ta ce mayakan sun yi yunkurin tserewa amma ba su yi nasara ba sakamakon luguden wuta da aka yi musu babu kakkautawa, lamarin da ya yi ajalin kwamadojin uku da mayakansu da dama.
Kazalika, rundunar sojin ta kai wasu hare-hare a kusa a yankunan Ali Sheritti da Kwatan Shallan da ke kusa da garin Kukawa, inda aka kashe wasu ’yan ta’addan na ISWAP da ba a tabbatar da adadinsu ba.