A wani samame da suka kai dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) sun yi nasarar hallaka wani babban jagoran kungiyar ISWAP, a yankin tafkin Chadi, Ammar Bin-Umar.
Majiya mai karfi na nuna cewar hatsabibin jirgin saman yakin nan na rundunar sojojin saman Najeriya wato Super Tucano ne ya kai harin tare da hadin gwiwar rundunar ta MNJTF.
- Ba za mu yaki ’yan bindiga da jiragen Super Tucano ba sai 2023 —Gwamnati
- 2023: Ganduje ya ki amincewa da ajiye aikin Kwamishinoninsa 3
Rundunar dai ta kunshi dakaru daga kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya.
Jiragen sun kai harin ne a maboyar ’yan ta’addan da ke Karamar Hukumar Marte ta Jihar Borno.
Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, kwararren masani kan yaki da ta’addanci cewa an kashe Bin-Umar ne a lokacin da yake yunkurin tserewa daga yankin na Tafkin Chadi.
Majiyar ta ce an kashe shi ne bayan shafe tsawon mako guda ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin, wadanda a baya suka kashe da ’yan ta’dda sama da 100, ciki har da kwamandoji goma.
Shi dai Kwamanda Bin-Umar yana daya daga cikin manyan ’yan kwamitin tattaunawa na Mujahidan na ISIS da aka tura yankin Khalifanci a watan Fabrairun 2022, don shiga tsakani sakamakon tsawaita yakin da ake yi tsakanin kungiyar Boko Haram da ISWAP.
Wakilan ISIS sun kuma zo ne domin sa ido kan kafa “Darul Quran”, sansanonin horar da masu tsattsauran ra’ayi a Kayowa da Kurnawa da Arge da Metele da Tumbum Allura, domin daukar ma’aikata, horarwa da shigar da yara mayaka.
Majiyar ta Zagazola ta fahimci cewa Cibiyoyin Darul ilmi da Darul Qur’an sun horar da daruruwan yara kanana sojoji a fagen yaki, ayyukan da ba na yaki ba, hada bama-bamai da fasahar yaki.
Har ila yau, wasu majiyoyin sirri sun ce ’yan kungiyar Boko Haram da ISWAP na cikin fargaba game da hare-haren da rundunar ta MNJTF ta kai a wasu maboyar tasu a Kananan Hukumomin Abadam da Marte a Jihar ta Borno.