Gwamnatin kasar Kamaru ta tsare wasu da ake zargi da kashe mutum tara ciki har da wata jaririya a yankin ’yan awaren kasar.
Sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce a ranar 1 ga watan Yuni ne lokacin da sojojin gwamnati hudu ke neman wani abokin aikinsu da ya bata, suka ci karo da mazauna yankin Missong wadanda suke fargabar za su kai musu hari.
- Mawaki Banky W ya lashe zaben Fid-da gwanin PDP a Legas
- NAJERIYA A YAU: Hakikanin Abin Da Ya Faru A Owo, Jihar Ondo
Ma’aikatar ta ce wannan ya sa sojojin suka bude wuta lamarin da ya yi sanadiyar hallaka mata hudu da maza hudu, da kuma jaririya ’yar wata 18, tare da raunata wata mai watanni 12.
Sanarwar ta bayyana matakin da sojojin suka dauka a matsayin wanda ya saba ka‘ida, musamman amfani da karfin da ya wuce kuma, abin da ya sa yanzu haka aka tsare su ana gudanar da bincike.
A watan Fabarairu 2020, sojojin kasar sun kashe mutum 23 lokacin da suka kai hari a kauyen Ngarbuh da ke Arewa maso Yammacin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce 15 daga cikin wadanda sojojin suka kashe kananan yara ne.