✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe dan ta’adda Ali Kachalla da kwamandojin Dogo Gide

Jiragen sojin Najeriya sun kashe dan bindiga Ali Alhaji Alheri, wanda ya jagoranci sace dalibai mata na Jami’ar Tarayya ta Gusau da kuma yaran Dogo…

Sojojin sama na Najeriya sun kashe kasurgumin dan bindiga, Ali Alhaji Alheri, wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje, wanda ya jagoranci sace dalibai mata na Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke Jihar Zamfara.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, cewa an kashe Kachalla Kawaje ne ranar Litinin a Jihar Neja.

Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 6 ga watan na Disamba, jiragen soji suka kai hari sansanin Ali Kachalla da Dogo Gide, suka kashe wasu gaggan ’yan ta’adda.

Wadanda aka kashe sun hada da Machika (kanin Dogo Gide, kwamanda a kungiyar Gide) da Dan Muhammadu, wani hatsabibin mai garkuwa da mutane a sansanin Dogo Gide.

Kasurguman ’yan bindigan uku tare da wasu da dama, an kashe su ne a lokacin da suke kokarin kai hari a Jihar Neja.

Aminiya ta ruwaito cewa Dogo Gide da Ali Kachalla sun addabi sassan jihohin Zamfara da Neja.