Rundunar sojojin Najeriya na ‘Operation Lafiya Dole’ sun yi nasarar kama wasu ‘yan kunar bakin wake biyu mata da ke da shirin kai hari a kauyen Mushemiri a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.
A rahoton da sojojin suka fitar a shafinsu na twitter na cewa, an kama wadanda ake zargin masu yin kunar bakin waken ne a daren ranar Laraba lokacin da suke yunkurin kai hari sansanin sojojin a bataliya ta 222 da ke jihar.
Matan da aka kama duk su na daure da bamabamai a jikinsu .