Sojoji daga barikin Mogadishu sun kama wani malamin addinin Muslunci da matarsa da ake kira Sheikh Muhammad Alkandawi a gidansa da ke unguwar Dei-dei a Abuja.
Tun da farko dai a wani sakon murya da Sheikh Muhammad Alkandawi ya saki ya bayyana cewa an kama matarsa da wasu almajiransa uku a ranar Asabar.
Ya ce, an sako almajiran nasa, amma sojojin sun ce sai ya zo za su saki matarsa.
Alkandawi ya ce, bai san alakar da ke tsakaninsa da sojojin ba, tun da shi ba mai satar mutane ba ne, ba kuma ɗan ta’adda ba ne.
- Matasa sun kori sarki daga fada
- Rikicin Sarauta: Alkalan Kano za su gurfana a Abuja kan umarni masu karo da juna
Malamin ya ce sojojin sun kira shi ta wayar matarsa, sai ya bukaci su haɗu da su a ofishin ’yan sanda da ke zuba, amma sun ki yarda.
Bayan wannan ne aka bayyana cewa malamin ya mika kansa gare su.
A baya dai malamin suna takun saka da wani mutum a kan wani fili da ke yankin.
Bayanai sun tabbatar da cewa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne sojoji suka sako abokin takaddamar malamin da ya kwashe kwanaki a hannunsu.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin sojojin da ’yan sanda, amma abin ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.