Sojojin rundunar Operation Hadin Kai OPHK a Jihar Yobe sun kama tabar Wiwi da kudinta ya kai Naira miliyan 4 da ake kyautata zaton za a kai wa ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ne da kan iyakar Najeriya da Jumhuriyar Nijar.
Kwamandan Ayyuka na rundunar, Birgediya Umar Muazu, ne ya tabbatar da hakan yayin da ya mika tabar wiwin ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) a Damaturu, hedikwatar Jihar Yobe.
- An tsinci gawar mace da aka yi gunduwa-gunduwa da ita a Indiya
- Matakin da za mu dauka bayan kotu ta sallami Nnamdi Kanu —Ministan Shari’a
Birgediya Umar Muazu ya ce dan aiken ya bar motar da ke dauke da kayan ya gudu a lokacin da ya hango dakarun da ke sintiri a yanki na kan iyaka.
Ya kara da cewa alamomi na nuna kayan tabar wiwin ana son ne a kai su Tungus, yankin ’yan ta’adda da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
“Babu wanda ake tuhuma da aka kama saboda dukkansu sun bar motarsu suka gudu bayan da suka hango masu sintiri suna kokarin cin masu.
“A cewarsa fataken na tabar wiwi suna kai kayan ne zuwa yankin ’yan ta’addan ne saboda abubuwan da suke sha ne ke sanya su aikata yadda suke yi domin babu wani mutum mai hankali da zai yi abin da suke yi ba tare da ya yi nadama ba.
“Don haka rundunar su ta samu nasarar kwace wadannan kaya kuma cikin ikon Allah muna kara kokari wajen murkushe wadannan ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas,” in ji Muazu.