✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun juyin mulki karo na biyu cikin watanni takwas a Burkina Faso

Sabuwar gwamnatin sojin ta dakatar da amfani da kundin tsarin mulkin kasar.

Sojoji sun sake juyin mulki karo na biyu cikin watanni takwas a kasar Burkina Faso da ke Yammacin Afirka.

Wani kyaftin din soji a kasar, Ibrahim Traore ne ya sanar da hambarar da gwamnatin da Laftanar Kanar Paul-Henri Damiba ke jagoranci a ranar Juma’a.

Kyaftin Traore ya ce wani rukuni na dakarun sojin da suka taimaka wa Damiba kwatar mulki a watan Janairun da ya gabata, sun yanke shawarar hambarar da gwamnatinsa saboda ya gaza magance masu ikirarin jihadi da suka addabi kasar da hare-hare.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito Kyaftin Traore yana ayyana dokar takaita zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safiya duk rana.

Haka kuma, sabuwar gwamnatin sojin ta ayyana rusa gwamnatin mai ci tare da dakatar da amfani da kundin tsarin mulkin kasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 24 ga watan Janairun wannan shekara ce Laftanar Kanar Damibda ya jagoranci hambarar da gwamnatin farar hula ta Shugaba Roch Kabore saboda makamancin wannan dalili.

Tun safiyar wannan Juma’ar aka shiga fargabar juyin mulkin bayan da aka jiyo karar harbe-harbe daga babban sansanin soja da kuma wasu unguwanni a Ougadougou, babban birnin kasar.

Haka kuma an ji karar wata fashewa a kusa da Fadar Shugaban Kasar, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

Lamarin da ya sanya sojoji sun mamaye muhimman wurare da kuma hanyar zuwa fadar shugaban kasa, suka kuma toshe hanyoyin shiga ofisoshin gwamnati da gidan talabijin din kasar wanda ya dakatar da aiki.

Nan take dai ba a san ko yunkurin juyin mulki ne ba ko a’a, amma lamarin na kama da juyin mulki da aka gani a wasu kasashen Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka cikin shekaru biyu da suka gabata.

Kazalika, Kamfanin Dillancin Labaran Faransa, ya ruwaito cewa ilahirin gidajen talabijin da na rediyo basa aiki a sassan kasar.

Galibi farar hula ne suka yi farin ciki da juyin mulkin bayan da suka gaji da gwamnatin farar hula ta tsohon Shugaba Roch Kabore da ta gaza magance rikicin ‘yan ta’adda da suka kashe dubban farar hula a cikin ’yan shekarun baya-bayan nan, tare da kwace yankuna da dama na Arewaci da Gabashin kasar.

A jawabinsa na farko bayan juyin mulkin na watan Janairun da ya gabata, Damiba, wanda galibi ake gani a bainar jama’a sanye da kaki da tabarau, ya yi alkawarin maido da tsaro.

Sai dai hare-hare a kasar da ke fama da talauci a Yammacin Afirka sun kara muni kuma sojojin na cikin rudani.

Jami’an sojan da suka bai wa Damiba goyon baya a watan Janairu, sun nuna takaici kan rashin samun ci gaba, a cewar majiyoyin tsaro.

A wannan makon wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kashe sojoji 11 a wani hari da suka kai kan ayarin motoci 150 dauke da kayayyaki zuwa wani gari a Arewacin Burkina Faso. Har yanzu ba a san inda farar hula 50 suke ba.

‘Yan bindiga sun toshe yankunan Arewacin kasar, lamarin da ya sa al’ummomin yankunan shiga tsaka mai wuya.