✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji Sun Harbe Dan Bindiga Da ya Addabi Kaduna

A wata musayar wuta da ’yan bindiga sojoji suka harbe takadarin dan bindigar

Sojoji sun harbe wani hatsabibin dan bindiga da ya hana al’umma sakat a yankin unguwar Kidunu da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

A wata musayar wuta da ’yan bindiga ce sojoji suka yi nasarar harbe takadarin dan bindigar, kamar yadda Kwamishinan Tsaron da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar a ranar Talata.

Aruwan ya ce, “Bayan musayar wutar, mun harbe wani dan bindiga, wanda daga baya muka gano ya yi kaurin suna da adddabar yankin.

“Mun kuma kwace bindigogi biyu kirar AK47 tare da layu da wayoyin hannu, da babura biyu”, in ji kwamishinan tsaron.

Ya bayyana cewa bayanan sirri suka samu cewa ’yan bindigar za su kai a garin hari a garin Kaduna da kewaye, sai suka tashi tawaga ta musamman ta tare su, suka yi musayar wuta.

Ya ci gaba da cewa, “Muna farin cikin sanar da al’umma cewa muna samun hadin kai daga gwamnati da sauran jami’an tsaro, musamman wajen samun bayanai da kuma aiki tare.

“Mu ma muna ba su bayanai yadda ya kamata, da kuma tattaro musu bayanan sirri da dukkan abin da ya dace”, in ji Aruwan.