✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun fatattaki ’yan ta’addan hanyar Kaduna-Abuja

Sojojin sun yi ruwan wuta a maboyar 'yan ta'addan da ke kai hare-hare a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Rundunar Sojin Sama ta ‘Operation Whirl Punch’ ta fatattaki ’yan ta’adda da dama a wani barin wuta da ta yi a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Daraktan yada labarai na rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya ce an fara aikin ne bisa bayanan sirri da ke nuna akwai wani kasurgumin dan ta’adda da aka fi sani da Boderi tare da dan uwansa Nasiru da sauransu a maboyarsu da ke kauyen Tsaunin Doka a yankin.

“Jirgin sojojin saman Najeriya karkashin Operation Whirl Punch sun ci gaba da kai hare-hare ta sama kan ‘yan ta’addar da ke shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, wanda ya kai ga halaka wasu ‘yan ta’adda a Tsaunin Doka da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Sanarwar ta kara da cewa, “Daga baya, an kai hare-hare ta sama a wurin da sanyin safiyar ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023, inda aka yi nasarar fatattakar da yawa daga cikinsu.

“An kuma kai harin wannan hari a maboyar ‘yan bindigar tare fatattakar Boderi. Dukkanin hare-haren biyu an yi nasara kuma an fatattaki ‘yan bindiga kuma an yi nasara.”

Air Commodore ya bayyana cewa Boderi da mukarrabansa suna da alhakin kai hare-hare da sace-sace da dama a hanyar Abuja zuwa Kaduna, hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, da kuma wasu yankuna a jihohin Kaduna da Neja.