Sojojin Najeriya a ranar Lahadi sun fatattaki mayakan Boko Haram da suka kafa wani shinge a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a jihar Borno.
Rahotanni dai sun ce sai da sojojin suka yi musayar wuta da ’yan ta’addan a kusa da garuruwan Minok da Jakana kafin su fatattakesun.
- Garkuwa da dalibai: Mafarautan Zamfara na neman a basu gadin marantun kwana
- Dalilin da zai sa mu rika amfani da kayan lambu a abincinmu na yau da kullum
Wani direba ya shaidawa Aminiya cewa lamarin ya faru ne jim kadan da sake bude hanyar da safe, wacce galibi ake rufeta da daddare.
A kan rufe hanyar ne kullum da yamma sannan a sake budeta da karfe 7:00 na safiyar kowacce rana.
A cewar direban, sojojin sun sami nasarar tarwatsa ’yan ta’addan ne bayan sun ci karfinsu a kokarin kafa shingen da suke yi a kan hanyar.
“Muna kan hanyarmu ta zuwa Maiduguri bayan mun kwana a Damaturu sai sojoji suka tsayar da mu a wani wuri bayan an wuce garin Mainok.
“Da farko an umarcemu mu koma, amma daga baya sai aka ce mu tsaya a inda muke. Daga nan ne sai muka jiyo karar bindigogi, alamar ana musayar wuta, bayan kamar mintuna 30 kuma sai aka ce za mu iya tafiya,” inji shi.
Ya kuma ce yanzu karin jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a kan hanyar.
Boko Haram dai ta mayar da babbar hanyar wani tarkon mutuwa inda ko a makon da ya gabata sai da ta sace wata amarya kafin daga bisani a kubutar da ita.
Lokacin da sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa su fara aiki dai, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya basu ‘yan makonni kadan domin su shawo kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.