✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Sojoji sun fatattaki ’yan Boko Haram daga hanyar Damaturu-Maiduguri

Tun farko maharan sun yi wa matafiya kwanton bauna a hanyar inda suka kona tireloli da kuma tankar

Sojoji sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram da dama tare da kwace manyan motoci uku a kan Babbar Hanyar Damaturu Zuwa Maiduguri.

Dakarun Rundunar Soji ta Operation Hadin Kai sun yi nasarar fatattakar ’yan Boko Haram din ne a kan hanyar kauyen Lawan Minari da ke tsakanin Maiduguri zuwa Damaturu bayan ’yan ta’addan sun tare hanyar suka yi.

Tun farko maharan sun yi wa matafiya kwanton bauna a hanyar inda suka kona tireloli biyu da wata tankar mai.

Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya a Yankin Tafkin Chadi, ya ce sojojin kasa da na sama ne suka kai dauki cikin gaggawa zuwa wurin domin murkushe ’yan ta’adda a yayin da suke tsaka da cin karensu babu babbaka.

Ya kara da cewa da ’yan ta’addan da suka ga isowar sojojin, sai nan da nan suka yi kasa a gwiwa, lura da yadda wasu daga cikinsu suka sauko daga manyan motocinsu, suka fara gudu don kada jirgin yaki ya jefa musu bam.

Majiyoyin sun ce an kashe da yawa daga cikinsu a yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Majiyar ta bayyana cewa an samu nasarar kwato manyan motoci guda uku da kuma makamai bayan wannan artabu.