✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga, sun kwato rokoki a Zamfara

Dakarun sojin sun yi nasara kwato roka daga hannun 'yan bindigar.

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta ‘Operation Hadarin Daji’, sun yi nasarar fatattakar ’yan bindiga da dama bayan wani samame da suka kai a kauyukan Kagara, Gidan Fadama, Gangara, Tseika, Malamawa da Zango Kamarawa a Kananan Hukumomin Talata Mafara da Shinkafi a Jihar Zamfara.

Aminiya ta gano cewa, a ranakun Talata da Laraba, sojoji sun fara aikin shara a kan sansanonin ’yan bindiga da a yankunan, inda suka yi artabu da ’yan ta’addan, tare da kashe da dama daga cikinsu, suka lalata sansanoninsu.

Sojojin sun kuma kwato rokoki, bindigar PKT guda, alburusai, bindiga kirar AK-47 guda uku tare da lalata babura 19 na ’yan ta’addan.

Sun kuma kai wani samame a yankin Dogon Awo-Lamba Bakura da ke Karamar Hukumar Bakura, inda suka dakile harin da ’yan bindiga suka kai a babbar hanyar zuwa Sakkwato.

A baya dai ’yan fashin dajin sun tare babbar hanyar Sakkwato zuwa Gusau da nufin sace matafiya, amma sai sojojin suka yi gaggawar zuwa wurin tare da korar su.