✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Geidam

Rahotanni sun ce sojojin Najeriya sun dakile wani harin da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a kan garin Geidam na jihar…

Rahotanni sun ce sojojin Najeriya sun dakile wani harin da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a kan garin Geidam na jihar Yobe ranar Litinin. 

An dai ba da rahoton jin harbe-harbe da safiyar ranar ta litinin kafin daga bisani komai ya lafa.

Wannan harin ya zo ne sa’o’i kadan bayan rundunar sojin sama ta Najariya mai aiki da rundunar Operation Lafiya Dole ta kai wa mayakan farmaki tare da kashe wasu manyan Boko Haram da wasu ’yan Boko Haram bangaren Kungiyar IS reshen yammacin Afirka wato ISWAP a garin Durbada da ke jihar Borno.

Wakilin Daily Trust a Damaturu ya samu rahoton cewa maharan sun shiga garin ta kudu daga kauyen Gumsa suka rika harbin duk wanda suka samu.

Hakan ya sa jama’a da dama suka yi kaura daga yankunansu zuwa wasu wuraren.

Tuni dai mutanen suka fara komawa garin na Geidam.

 

Jama’ar garin Geidam sun bayyana takaicinsu da irin wannan mummunan harin suna cewa, wannan shi ne karon farko da aka taba kai masu hari irinsa.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce, an kashe jigogin Boko Haram da dama lokacin da rundunar sojoji ta kai wani samame kan mayakan kungiyar.

Babban jami’in sashen yada labarai na hedkwatar tsaron Manjo Janar John Enenche,  ya ce rundunar ta lalata sansanin mayakan a ranar 17 ga Afrilu 2020 lokacin da suka yi arangama.