Mutum 94 da kungiyar Boko Haram ke rike da su a gabar Tabkin Chadi sun kubuta yayin da a ranar Alhamis aka mika su a hannun Gwamnatin Jihar Borno.
Rundunar hadaka ta kasashen da ke yaki da kungiyar a yankin Tabkin Chadi MNJTF, ita ce ke da alhakin wannan babbar nasara.
Malam Isa Gusau, hadimi na musamman ga Gwamna Babagana Zulum kan harkokin sadarwa, shi ne ya labarta hakan cikin sanarwar da ya fitar a birnin Maiduguri.
Ya ce daga wadanda abin ya shafa akwai maza 37 da mata 17 da kuma kananan yara da dakarun hadin gwiwar suka ceto bayan sun yi ba ta kashi da ’yan ta’addan.
Ya ce Kwamandan rundunar, Manjo Janar Ibrahim Yusuf, shi ne ya mika wa Gwamnatin Borno mutanen, yayin da Kwamishinan Shari’a, Kakashehu Lawan, ya karba a madadinta.