Sojoji a Jihar Filato sun damke wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne da kuma ’yan fashi kimanin su 33 yayin a garin Jos.
Yayin da yake gabatar da su ga manema labarai a ranar Juma’a, Shugaban Runduanr Operation Safe Haven, Manjo Janar Chukwuemeka Okonkwo, ya ce, an kama wadanda ake zargin ne a sassan birnin Jos, inda a nan ne ake ci gaba da samun karuwar ‘yan kungiyar asiri a baya-bayan nan.
- ’Yan sanda sun harbe ’yan fashi, sun cafke wasu 8
- A kori Fashola: Ba abin da ya yi a Arewa —NEF
- Hisbah ta hana ‘Black Friday’ a Kano
Okonkwo ya ce, a wuraren da aka kama su sun hada da kasuwar Terminus, layin Rwang Pam, Ginin Rochas, Titin Ahmadu Bello da Agwan Rukuba duk a Karamar hukumar Jos ta Arewa ta jihar.
Har-ila-yau, rundunar ta kama wani gungun ’yan fashin a kan titin Angul D-Maraban Jamma a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.
Okonkwo ya ce, yayin gudanar da aikin nasu daya daga cikin ’yan fashin ya rasa ransa saura kuma sun ranta ana kare yayin da suka ji karar bindiga.
Ya ce, an samu ’yan fashin da karamar bindiga kirar gida da harsasai da dama,.
Ya bukaci jama’a da su taimaka da bayar da rahoton duk wasu bata-gari da suke karya dokar kasa da gudanar da ayyukan ta’addanci a fadin jihar.