✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun cafke ‘masu kashe mutane’ a Binuwai

Akalla mutum 13 ne aka kashe bayan mahara kusan 20 sun far wa garin Ukpogo suna harbe-harbe

Sojojin rundunar Operation Whirl Stroke sun tsare wasu mutum bakwai bisa zarginsu da hannu a rikicin sarautar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 13 a gundumar Ukpogo da ke yankin Edikwu na Karamar Hukumar Apa ta Jihar Binuwai.

Akalla mutum 13 ne suka rasa yayukansu a ranar Litinin din makon jiya bayan ‘yan bindiga kusan 20 sun far wa Ukpogo suna harbi kan mai uwa da wabi.

Wasu majiyoyi sun ce sojojin da ke kula da yankin da abun ya faru sun cafke wadanda ake zargin a ranar Litinin dauke da muggan makamai bayan samun bayanan sirri.

Sun ce sojojin sun cafke jagoran ‘yan bindigar ne a kauyen Amoke tare da kama mutum biyar daga cikin bakwai din dauke da muggan makamai.

“Bayan mutanen sun shiga hannu ne daya daga cikinsu ya yi wa sojojin jagora zuwa maboyar miyagun a garin Ugbokpo inda suka kama karin mutum biyu”, inji majiyar.

To sai dai kwamandan rundunar, Manjo Janar Adeyemi Yekini ya ki cewa uffan a kan batun inda ya shawarci ‘yan jarida da su tuntubi shalkwatar tsaro don neman karin bayani.