Rundunar Sojin Najeriya ta buƙaci Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa da ta bankaɗo masu ɗaukar nauyin ta’addanci domin cafke su.
Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa ne ya yi wannan kira yayin da ya karɓi bakuncin Shugaban EFCC, Ola Olukoyede a wannan Juma’ar.
Ya ce wannan dabara ta tunkarar matsalar ta’addanci ta hanyar da ba ta buƙatar amfani da ƙarfin tuwo karbabbiya ko’ina a faɗin duniya.
Janar Musa ya ce lokaci ya yi da ya kamata hukumar EFCC ta fara amfani da karfin da doka ta bata wajen damko mutanen da ke da hannu a taimaka wa masu ta’addanci da kuɗaɗen.
Babban Hafsan Tsaron ya ce kamo wuyan masu taimaka wa ta’addanci da kuɗaɗen shi ne babban abin da zai kawo ƙarshen hare-haren a Najeriya, kasancewar ayyukan laifin basa tafiya idan babu kuɗi.
Musa ya kuma jadadda cewa rundunar sojin Najeriya ba ta goyon bayan cin hanci da rashawa, kuma ba za ta lamunci shigar sojoji cikin rashawa ba, don haka rundunar za ta bai wa EFCC duk haɗin kan da take buƙata.
A nasa ɓangaren, Shugaban EFCC ya ce babu wata hukuma da ba ta da gudunmawar da za ta bai wa Najeriya a fannin yaƙi da rashawa, don haka ya zama wajibi jami’an tsaro su san da wannan.
Ya kuma koka kan yadda ake samun cin hanci tsakanin jami’an tsaro, yana mai alakanta hakan da karuwar matsalolin tsaro a wasu lokutan.