✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun bindige mutum 3 a Binuwai

Rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) ta Sojin Najeriya ta bindige mutum uku a wani samame da ta kai a Jihar Binuwai. Hakan na zuwa ne…

Rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) ta Sojin Najeriya ta bindige mutum uku a wani samame da ta kai a Jihar Binuwai.

Hakan na zuwa ne bayan wasau jami’an tsaro sun kama mutum 20 a wani samame a Karamar Hukumar ta Katsina-Ala a ’yan kwanakin nan.

Shaidu sun tabbatar wa wakilinmu cewa sojoji sun yi awon gaba da sama da mutum 30 daga cikin masu zaman makoki a Kenvanger Mbatyula da ke Karamar Hukumar ranar 21 ga Nuwamba, 2020.

Wata majiya ta ce bayan ’yan kwanaki an tsinci gawar mutun uku an jefar da ake tunanin suna daga cikin masu zaman makokin.

“Akalla mutum 30 ne aka kama a wurin zaman makokin wani wanda ya yi hatsari da babur ya mutu a kan hanyar Gbise, Atumbe Kenvanger”, inji shaidan.

Sai dai kuma wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa gawarwakin da aka gani ba su da alaka da masu zaman makokin da aka tsare.

Wakilinmu ya gano cewa OPWS ta kashe mutum ukun ne a samamen da ta kai a yankin Katsina-Ala inda tsoson dan ta’adddan jihar (Terwase Akwaza, wanda aka fi sani da Gana) yake sheke ayarsa.

Masu zaman makokin kuma dakarun Rundunar Tsaro ta Musamman (Special Forces) ce suka tsare su.

“OPWS ta bindige masu manyan laifi uku ta kuma kwato makami guda daya”, inji wata majiyar soji.

Wakilinmu ya tuntubi Kwamandan OPWS, Manjo Janar Adeyemi Yekini amma ya ce ya tuntubni Sashen Yada Labarai a Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya.

Zuwa lokacin hada wanna rahoto kakakin ’yan sandan Jihar Binuwai, DSP Catherine Anene, ba ta kai ga amsa kiran da Aminiya ta yi mata ba.