✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji da dama sun ɓace bayan harin Boko Haram a Borno

Ana fargabar ko 'yan ta'addan sun yi garkuwa da wasu daga cikin dakarun sojin.

Harin da Boko Haram ta kai sansanin sojoji a Jihar Borno, ya sa wasu da dama sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba.

Harin ya faru ne a ranar Asabar a sansanin Forward Operating Base da ke Sabon Gari a Ƙaramar Hukumar Damboa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa wasu daga cikin sojojin sun ɓace, yayin da wasu kuma suka rasu ko kuma sun ji rauni.

’Yan ta’addan sun mamaye sansanin sojojin, inda suka lalata musu kayan aiki, kuma suka yi amfani da jirage marasa matuƙa wajen naɗar bayanan sansanin.

Dakarun da suka yi ƙoƙarin kai wa sansanin ɗauki, an kai musu hari ta hanyar dasa musu bama-bamai a kan hanya.

Duk da cewa ba a bayyana adadin waɗanda suka rasu ba, an gano ragowar gawarwakin dakaru sama da 12.

Sojojin ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba.

An shiga damuwa cewa wasu daga cikin sojojin da suka ɓace na iya yiwuwa an yi garkuwa da su.

Harin ya nuna yadda hare-haren Boko Haram ke ƙara tsanani, inda ’yan ta’addan ke amfani da jirage marasa matuƙa wajen leƙen asiri, wanda ke nuna yadda sula samu dabaru wajen kai hare-harensu.

A cikin makonni biyu da suka gabata, ’yan ta’addan sun yi amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hari a wani sansani a Wajiroko.