✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soji sun kama ‘yan bindiga a Kudancin Kaduna

Rundunar soji ta Operation Safe Haven ta kama ‘yan bindiga takwas da ake zargi da kashe-kashe a kauyukan Kudancin Kaduna. An kuma harbe daya daga…

Rundunar soji ta Operation Safe Haven ta kama ‘yan bindiga takwas da ake zargi da kashe-kashe a kauyukan Kudancin Kaduna.

An kuma harbe daya daga cikin ‘yan bindigar a kokarin kama su.

Kwamandan Rukunin Soji ta biyu, da ke kula da Kudancin Kaduna, Kanar David Nwakonobi, a lokacin gabatar da ‘yan bindigar a Kafanchan ya danganta nasarar kamo su da bayanin sirri na kwarai da aka ba su.

“Ranar 5 ga watan Agusta sojojinmu suka yi amfani da bayanan sirri na kwarai suka kamo wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne mutum shida a Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.

“Sojojin da taimakon ‘yan banga sun kuma kamo wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne a kauyen Chawai da ke tsakanin kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf”, inji kwamandan

Nwakonobi ya ce sun kama su da bindigogi kirar gida guda biyu samfarin (Pump Action Guns) da kananan bindigar Pistol biyu, su ma kirar gida da harsashi da adduna da sauran makamai.

Kwamandan ya ce za a mika su hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.

Nwakonobi ya kuma kara bayar da tabbacin za su ci gaba da aiki tare da mutanen garuruwan domin kawo karshen kashe-kashen da ake gama da su a yankin.