Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kai mayaka na musamman da karin dakaru da za su karfafa yakin da ake yi da ‘yan bindiga a Kudancin Jihar Kaduna.
Kakin rundunar tsaro Manjo Janar Enenche ya ce domin dakile farmaki da kisan dauki dai-dai da ake yi a Kudancin Kaduna, rundunar Operation Safe Haven ta kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi a yankin.
“Musamman aka kawo sojoji masu kwarewa ta musamma a wurare masu matsala a yakin.
“Wannan hanya ce da muke ganin za a samu nasara idan muka samu sahihan bayanai da bayanan sirri daga mutanen yankin.
“Saboda haka muke rokon al’ummomin yanki da su ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar ba mu bayanan da suka dace da za su taimaka wajen cimma manufarmu ta korar miyagu daga yakin”, inji shi.
Enenche ya ce sojin da ke gudanar da salon (Operation Hadarin Daji) suna ci gaba da fatattakar ‘yan bindigar daga Arewa maso Yamma.
Ya ce ta’adancin ‘yan bindiga da satar shanu a Jihohin Katsina da Kebbi da Zamfara da Sakkwato ya ragu na tsawon wata daya ke nan.
Enenche ya ce jami’an tsaro sun ci karfin ‘yan bindiga kuma zaman lafiya da huldodin yau da kullum sun fara dawowa a yankin.
Da yake bayani a kan Arewa maso Gabas, Enenche ya ce sojoji na ci gaba da samun galaba a kan ‘yan ta’adda.
Ya ce sojoji sun nuna wa ‘yan ta’adda karfin yaki da ya rage wa mayakan Boko Haram da ISWAP karfin yaki a yankin.
Ya kuma ce soji na ci gaba da sintitri da kai samame da farmaki tare da nemo bayanan sirri, ta hanyar amfani da mayakanta na sama da kasa a yankin.